Shugabannin ECOWAS sun gana da Gbagbo

Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo ya yi zaman dirshan

Wasu shugabannin kasashen Afirka uku sun gana da shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, domin shaida masa bukatar ya sauka daga mulki, salin alin ko kuma a tsige shi ta karfin tsiya.

Shugabannin uku da suka hada da na Benin, Saliyo da Cape Verde sun gana da Mr. Gbagbo ne a madadin kungiyar ECOWAS, wadda ke daukar Alassane Ouatara a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yii kwananan a kasar.

Ministan sadarwa na kasar Saliyo Ibrahim Ben Kargbo ya ce Tilas ne a ba Mr. Ouatara damar jan ragamar Ivory Coast kuma Laurent Gbagbo ya yarda da zabin jama'a.

Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya ce ganawar ta yi armashi, amma bai yi wani karin bayani ba.

Shi dai Mr Gbagbo ya nace kan cewa shi ne ya lashe zaben da ake takaddama a kai.

Majalisar tsarin mulkin kasar ce ta soke nasarar da Alassane Ouattara ya samu a zaben da aka yi ranar 28 ga watan Nuwamban da ya wuce ta hanyar kafa hujja da cewar an yi magudi a arewacin kasar, majalisar da wani na hannun-daman Gbagbo yake shugabanta.

Kakakin gwamnatin kasar Saliyo ya shai da wa BBC cewa tawagar shugabannin kasashe na kungiyar tattalin arzikin afirka ta yamma, ECOWAS za su bai wa Mr Gbagbo ne damar sauka daga kujerar mulki ne ba tare da an ci masa muntunci ba.