'Yan sanda a Denmark sun dakatar da harin 'ta'addanci'

Harin da aka kai a Denmark
Image caption Harin da aka kai a Denmark

'Yan sanda a Denmark da Sweden sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin suna shirin kai harin da mahukunta suka ce na ta'addanci ne.

'Yan sandan sun ce a binciken da suka yi sun gano bindiga mai sarrafa kanta da kuma albarusai.

Shugaban hukumar leken asiri ta kasar Denmark, Jakob Scharf ya ce sun gano cewa wannan wata kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ce da ke da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda na wasu kasashe ke yunkurin kai harin.

Mahukuntan kasar Denmark sun ce wasu daga cikin wadanda ake zargin 'yan kasar Sweden ne wadanda suka tsallaka cikin kasarsu