Bama-bamai sun tashi a jihar Bayelsa

Harin bam a Nigeria
Image caption Harin bam a Nigeria

Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a garin Yanegoa babban birnin jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Nigeria.

Bama-baman sun tashi ne yayinda wani dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyar PDP Mr Beemo Seiff ke yakin neman zabensa.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacinda 'yan takarar mukaman siyasa a jihohin Nigeria ke ta kokarin nuna irin bajintar su ga magoya bayansu, ganin yadda zabukan fidda gwani ke kara matsowa.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma, wasu bama-bamai sun tashi a garin Jos babban birnin jihar Pilato inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hakan dai na kara gaskata fargabar da wasu ke da ita na cewa, za a samu karuwar tashe-tashen hankula yayinda ake ci gaba da fuskantar zabubbuka a Najeriya.

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewacin Najgeria ma sun nuna cewar da misalin karfe bakwai na daren Laraba ma wasu 'yan bindiga sun sake kai hari a unguwannin Dala da Bulunkutu, inda suka kone daya daga cikin motocin sintiri na jami'an tsaro kurmus, bayan sun bude musu wuta.

Ko a daren Talata ma sai da 'yan bindigar suka kai hari a unguwar London Ciki, inda dan sanda guda ya rasa ransa, yayin da wasu mutane biyu kuma suka samu munanan raunuka.

Tuni dai Kungiyar Jama'atu Ahlil Sunna Lidda'ati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram suka yi ikirarin cewar su ke da alhakin kaddamar da hare-hare da kashe-kashen jami'an tsaro da masu unguwanni a birnin na Maiduguri tun kimanin watanni shidan da suka gabata.