'Yan sanda sun kama mutane 92 a Borno

Wasu 'yan sanda a Nijeriya
Image caption Wasu 'yan sanda a Nijeriya

Hukumomin 'Yan sanda a jihar Bornon Nijeriya sun tabbatar da cafke mutane casa'in da biyu, a wani samame da suka kai kan wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

A jiya ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram din ne suka kai hare-hare kan wasu wurare a birnin Maiduguri, inda suka kashe mutane ciki har da wasu 'yan sanda uku.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Muhammad Abubakar Jinjiri, ya shaidawa BBC cewa a iya saninsa mutane biyar ne aka kashe, da suka hada da 'yan sanda uku.

Alhaji Jinjiri ya ce suna ci gaba da bincike kan wadanda suka kama, ciki har da wani dattijo da suke zargin yana taimakawa 'yan kungiyar Boko Haram.