An sami tsohon shugaban Isra'ila da laifin aikata fiade

Moshe Katsav
Image caption Moshe Katsav

Wata kotu a birnin Tel Aviv ta sami tsohon shugaban kasar Isra'ila, Moshe Katsav, da laifuka biyu wadanda suka shafi yiwa wata mata da ke yi ma shi aiki fyade.

Har illa yau kotun ta same shi da laifin nunawa wasu mata biyu rashin da'a da kuma cin zarafin su.

Mai shigar da kara ta ce wannan hukuncin na yau, tamkar darasi ne ga wadanda ke amfani da mukaminsu wajen aikata ba daidai ba, kuma gani ga wane isa wane tsoran Allah.

Nan gaba ne za'a bayyana hukuncin da kotun ta yankewa Mr Katsav , amma hukuncin fyade mafi karanci a kasar shi ne daurin shekaru hudu a gidan kaso.