An sarewa wani matashi hannu a jihar Sakkwato

Barnar da tashin hankali ke haddasawa
Image caption Tashin hankalin siyasa na iya haddasa asarar dukiya har ma da rayika.

Yan sanda a jahar Sakkwaton Najeriya sun ce suna tsare da wani mutum da ake zargin ya sarewa wani saurayi hannu da adda.

Saurayin, Yahaya Bello, ya rasa hannunsa na hagu ne a wajen wani rikici tsakanin wasu yan bangar siyasa dake dauke da makamai a garin Wurno a lokacin wani gangamin siyasa a ranar Talatar da ta wuce.

Jahar ta Sakkwato dai ta sha fama da rikice-rikicen siyasa a yan shekarun nan wadanda suka haddasa salwantar rayukka da kuma raunata wasu mutane da dama.