Ambaliyar ruwa a Kasar Australia

Ambaliyar ruwa a kasar Australia
Image caption Fira Ministan kasar Australia na yin rangadi zuwa wasu yankunan da ambaliyar ruwa ya lalata a arewa maso gabacin kasar.

Fira Ministan Kasar Australia na yin rangadi zuwa wasu yankunan da ambaliyar ruwa ya lalata a arewa maso gabacin kasar, inda fiye da mutane dubu hudu suka rasa matsugunnasu.

An dai kwashe gabakidayan mutanen dake rayuwa a wasu garuruwa biyu a jahar Queensland.

Firimiyan jahar Anna Bligh yace bala'in ambaliyar ruwan zai lashe biliyoyin daloli, idan akayi la'akari da yadda amfanin gona ya lalace.

A waje daya kuma ana yiwa mutanen kudancin kasar Australian gargadin afkuwar wata gobarar daji a nan gaba, yayinda yanayin yankin yake kara yin zafi da fiye da makin digirin celcious arba'in da kuma iska mai karfi da take tasowa