Ra'ayi Riga: Ta yaya za a magance rikicin zabe a Afrika?

Laurent Gbagbo
Image caption Ya nuna ba zai sauka daga mulki ba

Zaben shugaban kasar da aka yi a kasar Cote d'Ivoire kusan wata dayan da ya wuce, ya bar baya da kura.

Bayan da sakamakon zaben ya nuna cewa dan takarar 'yan adawa, Alassane Ouatarra, shi ne ya samu nasara, amma daga baya kotun tsarin mulki ta kasar ta yanke hukuncin cewa shugaba Laurent Ggabgo ne ya lashe zaben.

A karshe dukkan 'yan takarar biyu dai sun rantsar da kansu a matsayin shugaban kasa.

An yi tashin hankali tare da asarar rayuka. An kuma irin wannan rigima tare asarar dimbin rayuka bayan zaben Kenya a 2007.

Nan gaba kadan ne kuma Najeriya, da Nijar da Kamaru ke shirin yin nasu zabukan.

To abin tambaya a nan shi ne, me haka ke nufi ga tafarki mulkin damokuradiya a nahiyar Afrika, kuma ta yaya za a kauce wa irin wannan sarkakiya?

Wannan shi ne abin da zamu tattauna tare da ku a wannan makon, a filinmu na Ra'ayi Riga.