An kai harin bom a Abuja

Jami'an tsaro a yankin da aka kai hari a Abuja
Image caption Jami'an tsaro a wurin da aka kai hari a Abuja

Hukumomi a Najeriya sun ce, akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayinda fiye da goma sha uku suka samu raunuka sakamakon wani bom da ya tashi a wata kasuwar sayar da barasa ta sojoji da ke barikin sojoji ta Mogadishu wadda aka fi sani da Abacha Barracks a Abuja.

Bom din ya tashi ne Juma'a da daddare a dai-dai lokacin da mutane da dama suka fara taruwa a kasuwar domin gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekarar 2011.

Tashe-tashen bama-bamai dai na son zama ruwan dare a Najeriya a 'yan kwanakin nan.

Ko a jajiberen ranar Kisimeti ma dai sai da wasu bama-baman suka tashi a Jos babban birnin jihar Pilato inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Bom din dai ya tashi ne a kasuwar da ke kimanin mita dari daga barikin Sojin yayinda mutane suka fara taruwa domin bukukuwan jajiberen sabuwar shekarar 2011.

Rudani

Jami'an'tsaro dai sun yi ta yekuwar jama'a su dauke motocinsu daga wurin sakamakon rudanin da ya biyo bayan tashin bam din.

Wani dan kasuwa da abin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa BBC cewa bam din ya tashi ne a wata rumfar da ake sayar da barasa. "Bai fi mintuna goma da na wuce ta wajen ba sai na ji wata kara, nan take wuta mai karfi ta tashi ta yi sama, mutanen da kafafuwansu suka yanke, mu muka taimaka aka sanya su a mota aka wuce asibiti da su. Mutane da dama ba su rurrufe shagunansu ba, kowa ya ranta a na kare ne."

An samu alkaluma masu karo da juna dangane da yawan mutanen da suka rasa rai ko jikkata a a lamarin.

Yayinda wasu majiyoyi ke cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu a hadarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan birnin Abuja Moshood Jimoh, ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu, yayinda 13 suka samu raunuka.

Duk da cewa babu wanda ya dauki nauyin kai harin, kuma hukumomin tsaro ba su fito sun bayyana ko su wa suka kai harin ba, sai dai shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin bom din, inda ya kara da cewa wadanda suka kai harin su ne suka kai harin bama-bamai a Jos a jajiberen ranar kirsimeti.

Bama-bamai

Hare-haren bama-bamai dai na neman zama ruwan dare a kasar.

Ko a ranar Larabar da ta gabata ma sai da wasu bama-bamai biyu suka tashi a wajen wani taron siyasa a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa, baicin harin bom da aka kai a Jos a jajiberen ranar Kirsimeti da kuma bom dinda ya tashi a filin taro na Eagle square a lokacin da kasar ke bukukuwan cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai a watan Oktoban da ya gabata.

Duka wadannan hare-haren na aukuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke tunkarar zabubbuka da za a gudanar nan gaba cikin shekarar nan, abinda ya sa wasu ke hasashen zai yi wuya ba a samu karuwar tashe-tashen hakula kafin zaben ba.