Harin Bam ba zai hana Najeriya ci gaba ba-Jonathan

Jonathan
Image caption Hari Bam ya zama ruwan dare a Najeriya

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya ce harin bomb din da aka kai zuwa wata kasuwa, dake kusa da barikin soja na Mogadishu, wanda aka fi sani da Abacha Barracks a Abuja, ba zai kawowa kasar tarnaki ba, a yunkurin da ta ke na ci gaba .

Shugaba Jonathan, ya ce wadannan hare hare ba zasu hana Najeriya dosar, inda ta sa a gaba ba.

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan dai ya ce wajibi ne a dukufa domin samar da kasa inda babu wani sarari ga masu aikata ta'addanci.

Shugaban a wani jawabi da yayi a wajen addu'o'in shiga sabuwar shekara a wani coci, ya sha alwashin kakkabe masu aikin ta'addanci a kasar inda yace harin ka iya fitowa daga wajen tsagerun naija delta ko kuma masu raayin rikau na addinnin musulunci a arewacin Najeriya.

Rundunar 'yan sanda ta ce mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hari a yayinda wasu mutanne n 21 ke asibiti amma dai akwai alkaluma ma bambamta akan adadin wadanda suka rasu.

Masu sharhi dai na ganin cewar duk bugun kirjin da shugaba Jonathan keyi na hukunta wadanda suka yi aika aikar, amma dai akwai shakku akan shiri da kuma karfin jamian tsaron kasar wajen murkushe ayyukan taadanci a nan gaba.