Ruwa ya malale wasu yankunan Australiya

Ambaliyar ruwa a Australiya
Image caption Ruwa ya malale yankunan Australiya da dama

A yayin da ambaliyar ruwa ta malale yankuna masu yawa na Jihar Queensland ta arewa maso gabashin kasar Australia, ana fargabar cewa cika da batsewar da teku ke yi, zata malale birnin Rockampton da ke gab da gabar tekun.

A halin da ake ciki, 'yan sanda na amfani da kwale-kwale wajen kwashe jama'a.

Magajin garin birnin Rockhampton ya gargadi jama'a cewar idan ta kama ko da karfi ne za a fitar da mutane.

An yi kiyasin za a yi asarar dumbin biliyoyin daloli a sakamakon wannan ambaliya.

Ma'ajin Jihar ta Queensland Andrew Fraser, ya ce, asara ba wai kawai ta gyare-gyaren da za a yi ba ne, da kuma asarar da gwamnati zata yi, wajen sake gina garuruwa da hanyoyi da gadoji ba, a'a har ma da asarar da sauran jama'a tafka.