FIFA zata binciki zargin almundahana

Sepp Blatter, shugaban hukumar FIFA
Image caption Sepp Blatter, shugaban hukumar FIFA

Shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya, watau FIFA, ya ce yana son kafa wani kwamiti wanda zai gudanar da bincike akan zargin cin hanci da rasha a cikin hukumar ta shi.

Jami'in, Sepp Blatter, ya ce makasudin wannan abu shine kara martabar hukumar a idanun duniya, tare da tabbatar da ana gudanar da aikace aikace a harkokin da suka shafi kwallon kafa ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba.

Wannan furuci nasa ya zo ne makwanni da dama bayan da hukumar ta FIFA ta dakatar da wasu wakilan kwamitin zartarwarta guda biyu akan zargin sun karbi toshiyar baki.

Dukkanin mutanen, sun musanta zargin da aka yi musu.

Wakilin BBC a Geneva, ya ce da wuya wannan yunkuri na hukumar FIFA ya kawo karshen kace-nace din da ake yi akan yadda ake gudanar da ita kanta hukumar.