Dokar hana busa Sigari a Spain

dokar hana busa sigari
Image caption Hana busa sigari cikin jama'a

Kasar Spain ta zartar da dokar hana shan taba sigari a bainar jama'a wacce tafi kowacce tsauri a nahiyar Turai.

Dokar ta haramta busa sigari a duk wuraren da jama'a ke taruwa da kuma daura da asibitoci, da filayen wasa ko makarantu.

Wakilin BBC Peter Nettleship ya ce jami'an wadannan wurare sun yi maraba da dokar sai dai da dama daga cikin masu gidajen giya da shagunan sayar da abinci na fargabar asarar cinikin da za su yi kafin al'ummar Spain su saba da wannan sabuwar doka.

Tun cikin shekarar 2006 dai aka haramta busa sigari a wuraren aiki sai dai likitoci na gargadin cewa a kullum mutane dari da sittin ne ke mutuwa a Spain sanadiyyar cututtukan da su ka danganci shakar hayakin sigari.