Arangamar Kiristoci da 'yan sandan Masar

zanga-zangar Kibdawa
Image caption Kibdawa masu zanga-zanga

Kiristoci kibdawa a Masar sun sake arangama da 'yan sandan kwantar da tarzoma, kwana guda bayan da wani harin bom a cocin da ke garin Iskandriyya ya kashe masu bauta ashirin da daya.

Daruruwan Kiristocin da suka gudanar da zanga-zangar a Iskandriyya da al-Qahira sun bukaci gwamnati da ta kara zage dantse wurin kare al'umarsu.

A birnin al-Qahira, masu zanga-zangar sun rika yiwa jami'an Masar da ke zuwa gaisuwa wurin shugaban cocin Kibdawa iya shege.

A garin Iskandriyya kuma kiristoci da dama sun halarci cocin da ya yi kaca-kaca da jini domin gudanar da ibada cikin fushi da alhini.

Mahukuntan Masar dai na binciken mutane da dama game da kai harin inda suke zargin wasu 'yan kasar waje da shirya makarkashiyar.