Shugabannin Afrika na neman Gbagbo ya sauka

Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo

Kasar Saliyo ta tabbatar tawagar shugabannin Afrika da za ta ziyarci Ivory Coast a yau za ta bukaci shugaba Laurent Gbagbo da ya sauka daga kan mulki ne ba tare da wata tattaunawa ba.

Ministan yada labarai na Saliyo Ibrahim Ben Kargbo ya shaidawa BBC cewa tawagar da ta kunshi shugabanni daga ECOWAS da kuma firaministan Kenya Raila Odinga daga gamayyar kasashen Afrika za ta samawa Mr. Gbabgo hanyar da zai bar mulki ne.

Yace; "A baiyane take cewa gamayyar kasashen Afrika, da majalisar dinkin duniya da ECOWAS da ma kowa da kowa duk sun ce wajibi ne ya bar mulki kuma wannan shi ne matsayar ECOWAS."

Kasashen duniya dai sun amince da abokin hamayyar Mr. Gbagbo Alassane Ouattara, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a baya-bayan nan.