An tabbatar da kisan gilla a Ivory Coast

magoya bayan Gbagbo
Image caption 'Yan bangar Gbagbo

Jami'in majalisar dinkin duniya da ke binciken zarge-zargen keta hakkin bil adama a Ivory Coast ya ce ya na da hujjar ana cigaba da kisan gilla a cikin makonnin da suka biyo bayan zaben shugaban kasar.

Simon Munzu ya shaidawa BBC ma'aikatansa sun tabbatar da faruwar wasu daga cikin kashe-kashen yayinda su ke cigaba da samun rahotanni daga iyalan wasu mamatan.

Mr. Munzu ya ce sau biyu jami'an tsaron Ivory Coast na hana jami'ansa bin bahasi kan rahotannin kisan kiyashi da aka ce an yi a wani kauye da ake kira Anyama, inda aka bada labarin ganin gawarwaki masu yawa da wasu suka kiyasata za su kai tamanin.

Ya kara da cewa kodayake akwai rahotannin da ke nuna an fi kai hare-haren kan wasu kabilu, karin gishiri ne idan aka ce wannan alamu ne na somi-somin kisan kare dangi.