Mutane tamanin sun mutu a tekun Yemen

Irin kwale-kwalen da ake hawa zuwa Yemen
Image caption Mutane sun mutu a tekun Yemen

Mahukuntan kasar Yemen sun ce wasu bakin haure 'yan nahiyar Africa akalla tamanin ne suka mutu a cikin tekun Yemen a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Yemen ta ce dukkanin kwale-kwale biyun da bakin hauren ke amfani da su, sun nutse a cikin Bahar Maliya ne, saboda iskar da ake fama da ita mai karfin gaske.

Har yanzu dai babu cikakken bayani, to amma gwamnatin ta kasar Yemen ta ce a yanzu haka tuni jami'ai masu aiki a gabar teku sun fara gudanar da bincike domin gano ko akwai wadanda ke da rai.

Dubban 'yan Afirka ne ke yunkurin zuwa kasar ta Yemen a duk shekara don samun ayyukan yi.