Jam'iyar CPC ta zabi Janar Buhari a matsayin dan takararta

Janar Muhammadu Buhari
Image caption Janar Muhammadu Buhari

Jam'iyyar CPC ta tsayar da Janar Muhammadu Buhari mai ritaya a matsayin dan takarar shugaban kasarta a zabe mai zuwa.

Jam'iyyar ta dauki wannan mataki ne a babban taronta na kasa baki daya a dandalin Eagle Square.

Wannan dai shine karo na ukku da Janar Muhammadu Buhari zai yi takarar shugabancin Nigeria. A can baya, Janar Buhari ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarun 2003 da 2007 a karkashin inuwar jam'iyyar ANPP.

Janar Muhammadu Buhari ya taba shugabancin gwamnatin mulkin soji a Nigeria tsawon watanni kamar 20 gabanin wata gwamnatin mulkin sojin ta yi masa juyin mulki.