Girka na shan suka game da gine iyaka

Bakin Haure
Image caption Bakin haure a Girka

Kasar Girka na shan suka game da shirinta na gina katanga a kan iyakarta da Turkiyya domin tare dubunnan bakin haure da ke tsallaka iyakar.

Hukumar tarayyar Turai ta ce gina katanga zai maganin matsalar na gajeren zango ne kawai yayinda kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce katangar za ta tilastawa masu hijira neman wasu hanyoyi ne na shiga Turai.

Wariyar launin fata dai na karuwa a Girka kuma ministan tabbatar da zaman lafiyar al'umma Christos Papoutsis ya yi watsi da sukan, inda ya ce kasar ba za ta iya ci gaba da karbar bakin haure ba.

A bara dai kimanin bakin haure dubu dari da ashirin ne suka shiga Girka daga Turkiya, inda mafi yawansu suka kara kutsawa cikin kasashen Turai.