Shugabannin Afrika sun gaza tursasa Gbagbo

Laurent Gbago
Image caption Gbagbo ya ki sauka

Tawagar shugabannin Afrika ta gaza tursasa Laurent Gbagbo ya sauka daga mulkin Ivory Coast cikin lumana bayan shafe yini guda tana ganawa da shi.

Wakilin BBC a Abidjan John James ya ce Mr. Gbagbo ya ki yarda da tayin da suka yi masa na samun kariya daga tuhuma, da tsaron lafiyarsa da dukiyarsa, tare da ba shi mafaka a wajen kasar idan ya sauka daga mulki.

Yanzu dai tawagar za ta koma ga kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika wacce tuni ta yi barazanar tunbuke Mr. Gbagbo da karfin tsiya idan ya ki yarda da lalama.

Tawagar ta kuma gana da Alassane Ouattara, wanda kasashen duniya ke ganin shi ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a Ivory Coast din, inda ya ce yanzu an kure duk matakan da za'a dauka ta fuskar diplomasiyya.