Jami'yyun siyasa da gwamnati na taro a Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

Majalisar CNDP, mai sasanta rikicin siyasar Nijar, ta yi taron gaggawa a yau, a kan wasu matsalolin da suka kunno kai, a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben kananan hukumomi.

Matsalolin dai sun hada da watsin da kotun tsarin mulkin kasar ta yi, na takardun neman 'yan takarar wasu 'yan siyasa, a zaben majalisun kananan hukumomin da kuma batun ingancin kundin masu jefa kuria, wanda wata kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci ta yi zargin cewa akwai sunaye da dama na bogi a cikin rejistar.

A ranar Asabar mai zuwa ce ake shirin gudanar da zaben kananan hukumomin.

Wasu 'yan siyasar ma nema suke a dage zaben, saboda a cewarsu, akwai wasu gyare -gyaren da ya kamata a yiwa rajistar masu zaben.