An kashe wani gwamna a Pakistan

Salman Taseer
Image caption Salman Taseer

An harbe gwamnan lardin Punjab na kasar Pakistan, Salman Taseer har lahira a Islamabad, babban birnin kasar.

'Yan sanda sun ce daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ne ya harbe shi a lokacin da ya fito daga cikin motarsa a wata babbar kasuwa.

Wakilin BBC ya ce, yayin da Pakistan ke fuskantar rikicin siyasa, sai ga shi an kashe wani jigon dan siyasar kasar a Islamabad.

Salman Taseer na daya daga cikin manyan 'yan siyasa a Pakistan, inda kwanan nan ya dauki hankalin jaridun kasar, bayan da ya roki shugaban kasar da yaiwa Asia Bibi wadda kiristace afuwa, bayan da aka yanke ma ta hukuncin kisa bisa sabon da ta yi.