An rantsar da sabuwar majalisar dokoki a Amurka

Majalisar Dokokin Amurka
Image caption Akwai babban kalubale a gaban Shugaba Obama

An rantsar da sabuwar majalisar dokokin Amurka a Washington, watanni biyu bayan zaben tsakiyar waadi, wanda jamiyyar shugaba Obama ta Democrats ta sha babban kaye a hannun jamiyyar Republican.

Jamiyyar Republican ta samu nasarar karbar ikon majalisar wakilan kasar a karon farko cikin kusan shekaru hudu, inda za ta nada sabon kakakin majalisar wato John Boehner.

John Boehner, sabon kakakin majalisar wakilan Amurkar, ya ce, "Babban abinda nake gani shi ne aikin kakakin majalisa shi ne, na kare tsarin mulki.

"Kuma na san cewa yawancin yan Amurka sun yi imanin cewa majalisar dokokin ta rabe.

Lokaci ya yi da za a dinke ta. Don haka wannan ne babban abinda zan baiwa muhimmanci."