Da hannun 'yan siyasa a hare haren Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Rundunar 'yan sandan jahar Borno ta danganta hare-hare da kashe-kashen da ake a birnin Maiduguri na baya bayan nan da 'yan siyasa.

A cikin hira da BBC, kwamishinan 'yan sandan jahar, Mohammed Jinjiri Abubakar, ya ce wannan ya biyo bayan irin binciken da suka gudanar, da kuma yanayin hare haren da ake kaddamarwa.

Ya ce sun kama mutanen da suka hada da 'yan bangar siyasa.

Haka kuma rundunar 'yan sandan ta ce ta cafke wani babban mutum, Alhaji Bunu Wakil, wanda take zargi da taimakawa 'yan kungiyar Boko Haram.

Kimanin watanni shidda kenan da masu kishin Islamar su ka kaddamar da hare hare a birnin Maiduguri.