'Gbagbo ba shi da zabi sai sauka', inji Odinga

Shugaba Laurent Gbagbo
Image caption Shugaba Laurent Gbagbo

Firayim ministan Kenya, Raila Odinga, ya ce yana ganin shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo, ya fuskanci ba shi da wani zabi face ya sauka daga kan mulki.

Mista Odinga, wanda ya wakilci Tarayyar Afirka a wata ganawa a kasar ta Ivory Coast, ya ce a shirye Mista Gbagbo ya ke ya tattauna kan yadda za a kawo karshen rikicin kasar cikin maslaha.

“Ina ganin ya fahimci cewa ruwa ya karewa dan kada kuma ba shi da wata mafita illa sauka daga kan mulki”, in ji Mista Odinga.

Sai dai kakakin mutumin da duniya ta amince cewa shi ya yi nasara a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Nuwamban bara, Alassane Ouattara, ya shaidawa BBC cewa babu wani abu da za a tattauna har sai Mista Gbagbo ya amince da sakamakon zaben.

Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, da Kawancen Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, sun ce a shirye su ke su yi amfani da karfin soji in dai Mista Gbagbo ya ki amincewa ya sauka daga mulki.