An yiwa majalisar ministocin Ghana garambawul

John Atta Mills, shugaban Ghana
Image caption John Atta Mills, shugaban Ghana

Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills, ya yi wa majalisar ministocin sa babban garambawul.

Wasu mambobin gwamnati biyu sun rasa mukamansu - wato ministan ilimi, Mr. Alex Tetteh Enyo, da ministar kula da yawon bude ido, Mrs Zita Okaikoi.

A karkashin garambawul din an kuma sauya wa wasu ministocin mukamai. Ministar shari'ar kasar, kuma Atoni Janar, a yanzu ita ce za ta shugabanci ma'aikatar ilimi.

'Yan adawa a Ghanar na ganin cewa, gwamnati tayi garambawul din ne a daidai wannan lokacin, domin kawar da hankalin jama'a daga karin kudin da ta yi wa man petur a kwanan nan.

Sanarwar da fadar gwamnatin Ghanar ta bayar, ta ce a nan gaba za a kara yiwa majalisar ministocin gyaran fuska.