Ana daf da gano maganin sanko

Ana daf da gano maganin sanko
Image caption Ana daf da gano maganin sanko

Masana a Amurka sun ce sun gano abin da ke haifar da wani nau'i na sanko.

Masanan sun wallafa sakamakon binciken da suka gudanar ne a wata mujalla mai suna Clinical Investigation.

Fiye da rabin mazan da suka haura shekaru hamsin a duniya ne dai ke da wani nau'i na sanko.

Wadansu mazan kuwa su kan fara sanko ne tun suna shekaru ashirin da haihuwa.

To amma masana sun ce suna daf da gano maganin sanko bayan sun fahimci abin da suka yi amanna shi ne ke haifar da sankon.

Kungiyar masanan na Amurka ta ce ta gano tushen matsalar a cikin mabubbugar gashi ta hanyar yin nazari a kan mutanen da ake yiwa dashen gashi.

A nan ne suka ce sun gano wadansu kwayoyin halitta masu tawaya wadanda gashin da suke samarwa ya yi kankanta ta yadda ba za a iya ganinsu ba sai da madubin da ke kara girman abubuwa.

Masanan na Jami'ar Pensylvania sun yi amanna cewa za a iya magance sanko ta hanyar tayar da komadar wadannan kwayoyin halittar.