An yi jana'izar gwamnan Punjab a Pakistan

Pakistan
Image caption Wani mai jimami yana kwance a kasa a lokacin jana'izar Salman Taseer

An yi jana'izar gwamnan yankin Punjab Salman Taseer a birnin Lahore na kasar Pakistan, bayanda aka kashe shi a ranar Talata.

Daya daga cikin masu tsaron lafiyar Mr Taseer ne ya harbe shi, saboda adawar da yake nuna wa da tsarin hukuncin kisa kan wanda ya aikata babban sabo.

Dubban jama'a ne suka taru a birnin Lahore domin jana'izar ta Mr Taseer, daya daga cikin 'yan siyasar Pakistan da aka fi jin kansu a kasar wanda kuma akewa kallon mai sassaucin ra'ayi.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta bayyana mutuwarsa da cewa "babban rashi ne", domin a cewarta ya taimaka wajen samar da zaman lafiya.

Gwamnan - wanda babban jami'i ne a jam'iyyar PPP mai mulkin kasar - ya sha suka daga masu gwagwarmayar addini bayanda ya nemi a yi wa wata mace kirista afuwa, bayanda aka yanke mata hukuncin kisa kan aikata babban sabo.

Zaman makoki

Fira Ministan Pakistan Yousuf Raza Gilani ya bayyana zaman makoki na kwanaki uku, sannan ya yi kira da a kwantar da hankali.

Sai dai, shugabannin addini sun yi maraba da kisan gwamnan, sannan suka yi kira da a kauracewa jana'izar, a cewar wakiliyar BBC a birnin Islamabad Orla Guerin.

Kimanin malaman addini 500 daga darikar Barelvi ta 'yan Sunni, sun bayyana cewa duk wanda ya nuna jimami kan mutuwar to shi ma zai fuskanci sakamako makamancin na Mr Taseer. "Kada wani musulmi ya halarci jana'izar ko ya nuna damuwa ko jimami ko addu'a ga Mr Taseer kan abinda ya same shi," a cewar Jamaat-e-Ahl-e-Sunnat Pakistan.