Rikicin cikin gida a PDP na kara kamari

Tambarin jam'iyyar PDP
Image caption Tambarin jam'iyyar PDP

A Najeriya, rikicin cikin gidan da ke addabar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar a jihohi daban-daban na ta kara zama gagarumar matsala, sakamakon yadda ake ta samun tashin-tashina dangane da zabubbukan shugabannin rassan jam'iyyar na jihohi.

Misali, a Jihar bauchi wadansu ’ya’yan jam’iyyar sun yi zargin cewa an tafka magudi a zaben fitar da wakilai da na ’yan takarar majalisar dokoki ta jihar; zargin da shugabannin jam’iyyar na jihar suka musanta.

A Jihar nasarawa kuwa, har hatsaniya wadansu matasan jam’iyyar suka tayar saboda abin da suka kira kakaba ’yan takara a kan ’ya’yan jam’iyyar.

A Jihar Enugu kuma, batun zaben shugabannin jam’iyyar na jiha ne ya haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin magoya bayan bangaren Gwamna Sullivan Chime da magoya bayan bangaren shugaban jam’iyyar na kasa, Okwesileze Nwodo.

Bangaren gwamnan dai ya ce zaben shugabannin jam’iyyar da bangaren shugaban jam’iyyar na kasa ya gudanar ya saba doka, kum bata lokaci ne kawai.

To amma bangaren shugaban jam’iyyar ya ce daya bangaren ba shi da wata hujjar cewa zaben ya saba doka; a cewarsu, kotu ce kawai za ta iya yanke hukunci a kan hakan.

Wasu masu lura da al'amura na ganin ire-iren wannan takaddama na iya hana jam'iyyar nasara a zaben da ke tafe; to amma uwar jam'iyyar ta musanta wannan hasashe.