'Yan Burtaniya na ci gaba da shiga addinin musulunci

A'isha Uddin
Image caption A'isha Uddin ta ce rayuwarta ta sauya tun da ta shiga addinin musulunci

A'isha Uddin 'yar shekaru 22 na daya daga cikin fararen fata 'yan asalin Burtaniya da ke kara rungumar addinin musulunci, kamar yadda wani bincike na jami'ar Swansea ya nuna.

A'isha na karanta Suratul Al-Fatiha a Alkur'ani mai tsarki - a gida tare da wata kawarta Sameeah Karim, tana dan samun cikas amma dai tana kokari.

Ba kamar Sameeah ba, 'yar shekaru 35, 'yar asalin kasar Pakistan, A'isha bakuwa ce a wannan fage.

A baya ana kiranta Laura, kuma ta shiga Musulunci ne shekaru biyu da suka wuce.

Fara ce; 'yar asalin birnin Birmingham, kafin yanzu tana shiga irin wacce 'yan matan Burtaniya ke yi.

'Sauyi ne mai ban mamaki'

Tace: "A baya ina saka dogon wando da kananan kaya sannan nayi kwalliya sosai".

A yanzu A'isha na saka dogon hijabi tare da doguwar riga mai kauri kamar yadda addinin musulunci ya umarta.

Image caption Sarah Joseph ta shiga Musulunci tun tana yarinya karama

"Wannan sauyi ne mai ban mamaki, amma ina farin ciki da aiwatar da shi", saboda ba na bukatar na bayyana tsiraici na ga jama'ar da ke kan titi.

A'isha ta fara sha'awar addinin musulunci ne a makaranta - sannan ta fara ziyartar masallacin unguwarsu a boye domin neman karin ilimi.

Tace ta shafe shekaru da dama tana bincike kan musulunci kafin ta mika wuya, inda ta sauya yanayin shigarta, sannan ta fara yin sallah sau biyar a kowacce rana.

"Rayuwata ta sauya, da ni takadara ce, ina yawan haifar da matsala a gida, ina fita yawo - ba na kokari a makaranta.

"Amma lokacin da na karbi musulunci sai nutsuwa ta zo mini. Ina zama a gida domin yin karatu a intanet da litattafai. Ina murna da halin da nake ciki yanzu, ina alfahari da kaina a yanzu domin na samu asali mai kyau".

Binciken jami'ar Swansea

Masu binciken na jami'ar Swansea sun ziyarci masallatai 250 a Burtaniya, inda suka gano cewa akwai mutane dubu 100 da suka shiga musulunci daga bangarori daban-daban a Burtaniya.

Wannan ya nuna an samu karuwa sosai idan aka kwatanta da mutane dubu 60 da suka shiga musulunci a shekara ta 2001.

Yawancin 'yan matan da aka tattauna da su, sun nuna cewa suna fuskantar kalubale da dama daga danginsu, inda ake musu kallon suna kaurace wa asalinsu.