Yara sun shaki dalma mai guba a China

Firimiyan kasar China Wen Jiabao
Image caption An garzaya da wasu yara kanana fiye da ashirin zuwa wani asibiti a kasar China bayan sun shaki dalma mai guba

An wuce da wasu yara kanana su ashirin da hudu zuwa wani asibiti dake wani kauye a gabashin kasar China bayan sun shaki dalma mai guba.

Kamfanin dillancin labaru na kasar wato Chinhau ya ce gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla yara dari biyu cikinsu harda jinjiri mai wata takwas, na dauke da gubar a cikin jinin su.

An dai yi amannar cewa wasu masana'antun kera batura ne a kauyen Anne- hue ke fitar da dalmar mai guba, amma tuni an rufe su.