Zaben cike gurbin gwamna a jihar Delta

Shugaban Hukumar zaben Nijeriya, Profesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar zaben Nijeriya, Profesa Attahiru Jega

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, wato INEC tana gudanar da zaben cike gurbin gwamnar jihar Delta, dake Kudu maso Kudancin kasar.

Zaben dai da Hukumar ke gudanarwa, ana yinsa ne sakamakon soke zaben da aka yiwa Dr Emmanuel Uduaghan a matsayin gwamnan Jihar Delta, a shekarar dubu biyu da bakwai, a bisa dalilai na rashin inganci.

Kusan 'yan takara goma sha hudu ne dai ke fafatawa a wannan zabe.

Wannan zaben dai tamkar zakarar gwajin dafi ne ga hukumar zaben kasar wajen gudanar da ingantaccen zabe, gabanin zabukkan da zaa yi a cikin watan Afrilu mai zuwa.