Kamfanin Renault ya dakatar da manyan jami'ansa

samfurin motocin  Renault
Image caption Kamfanin ya yanke shawarar ne domin kare muhimmiyar baiwarsa ta fasaha da basira

Kamfanin kera motoci na Renault ya ce ya dakatar da manajoji 3 saboda kwarmata wasu asirai 3 da ya ke kwaf-kwaf da su a kan sabuwar motarsa mai amfani da karfin wutar lantarki.

Kamfanin ya ce an yanke shawarar ne domin kare muhimmiyar baiwarsa ta fasaha da basira.

A wata alama ta muhimancin da aka dora a kan sabuwar fasahar, ministan masana'antu, Eric Besson ya ce kasarsa na fuskantar yakin tattalin arziki.

A daidai lokacin da fasahar kyare-kyare ke kara bunkasa a duniya, ana ci gaba da neman hanyoyin kyara motocin da ke amfani da makamashin lantarki, wacce za ta yi gogayya da mai amfani man fetur da aka saba amfani da ita. Kamfanin kyara motoci na Renault na daukar batun da mahimmanci. Mataimakin shugaban kamfanin Christian Husson, ya ce kamfanin ya kaddamar da bincike kan bayanan sirrin da aka tsaigunta.

A yanzu dai babu tabbas kan irin fasahar da aka fitar, ko sababbi ne ko kuma an mikasu zuwa wani wuri.