Ana nuna shakku kan rijistar masu zabe a Najeriya

Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben na fuskantar kalubale da dama

A Najeriya, jama'a na nuna shakku kan shirin da Hukumar Zabe za ta fara na rajistar sunayen masu kada kuri'a a duk fadin kasar.

Wannan shiri dai ya zo ne yayin da akasarin jama'ar kasar ke kallon batun rajistar sunayen masu kada kuri'a a matsayin wata cika ka'ida kawai.

Domin a ganinsu hakan ba ya yin tasiri wajen tantance adadin mutanen da za su kada kuri'a a rumfar zabe, ko ya fayyace ainihin wanda ya sami nasarar zabe.

Wakilin BBC a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed wanda ya duba tunanin jama'ar kasar, dangane da shirin sabunta rajistar masu kada kuri'ar, ya ce abin ya dade yana ciwa 'yan kasar tuwo a kwarya.

Nuna shakku

Idan akwai wani muhimmin abu da mafi yawa-yawan 'yan Najeriya ke kuka da shi, tun a farkon shirye-shiryen zabubbukan kasar, galibi ba wuce batun tanadin kundin sunayen masu kada kuri'a ba.

Sakamakon yadda suke zargin ba a yin abin da ya kamata, yadda ya kamata. Al'amarin da ya karya wa jama'a da dama kwarin gwiwa game da batun zabe a kasar shekara da shekaru.

To, sai dai wannan karon gwamnatin tarayya da Hukumar Zabe ta kasar, duk suna ta nannagen bayar da tabbaci cewa, za a ga sauyi mai inganci, tun daga matakin tsara kundin sunayen masu kada kuri'ar.

Har ma an daura damarar fara sabunta kundin nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Shin ko ya zuwa yanzu tunanin jama'a ya sauya game da yadda suke kallon al'amarin? Mista Petrus Obi, wani mai lura da al'amuran yau da kullum, cewa ya yi kayya: "Mun jijji alkawura da dama iri-iri, muna so mu gani a kas. A yanzu dai kam, ba a jawo hankalin 'yan Najeriya ta yadda za su yi amanna da abin da ake kokarin yi ba tukun.

"Kome zai bayyana ne yayin da muka ga an fara aikin tsara kundin sunayen masu kada kuri'ar, da kuma yadda ake gudanar da shi. Amma kuma duk da irin wannan ra'ayi mai tattare da dari-dari da wasu ke bayyanawa, akwai wadanda suka yi amanna da alwashin da ake ta yi game da shirin sabunta kundin sunayen masu kada kuri'ar.

Har ma suna dokin ganin an fara shi. Kamara yadda Joel Aniegbo, wani matashi ya bayyana:

"Tabbaci hakika, zan je a yi mani rajista idan aka fara aikin sabuntawar. Ta yadda zan zabi shugabannin da nake ra'ayi a zaben da ke tafe".

Ko ma dai mene ne tunani da ra'ayin jama'a game da shirin sabunta kundin sunayen masu kada kuri'ar, fatan 'yan Najeriya wannan karon daya ne.

Mista Frank Agu Kalu, wani mai fafutukar kare hakkin bil'Adama, ya fayya ce shi karara: "Fatanmu kuma abin da muke hankoron gani shi ne, a sama mana kundin sunayen masu kada kuri'a wanda aka tsara yadda ya kamata, sahihin kundi, wanda za a iya gaskatawa". Masu lura da al'amura na ganin idan har wannan fata ya tabbata, tabbaci hakika za a karfafa wa jama'ar Najeriya gwiwa game da fitar su kada kuri'a a lokutan zabe.

Har ma a yo zawarcin mutanen da suka saduda cewa, harkar zabe a Najeriya dodorido ce kawai.