Dimbin 'yan Ivory Coast na kwarara cikin Liberia

Wasu 'yan gudun hijirar Ivory Coast
Image caption Wasu 'yan gudun hijirar Ivory Coast

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce, zata bude wani sabon sansani a kasar Liberia, domin dubban 'yan gudun hijirar Cote d'Ivoire, wadanda ke ci gaba da tsallaka iyaka, suna kwarara zuwa can.

Wani kakakin hukumar a Liberiar ya ce, kimanin 'yan Cote d'Ivoire dubu ashirin da ukku ne suka nemi mafaka a kauyaka masu nisa a yankin, tun bayan barkewar rikici a kan zaben kasar.

Wakiln BBC ya ce 'yan gudun hijirar na goyon bayan bangarorin siyasa biyu, masu hamayya da juna a Cote d'Ivoire. Amma kawo yanzu suna zaman lafiya da juna a wuraren da suka warwatsu.