Za'a tura karin dakaru zuwa Ivory Coast

Sojin kiyaye zaman lafiya a kasar Ivory Coast
Image caption Babban jami'in aikin wanzar da lafiya na majalisar dinkin duniya a kasar Ivory Coast zai bukaci karin dakaru zuwa kasar

Shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya a kasar Ivory Coast , Alan Lee Roy ya ce yana da anniyar ganin cewa ya nemi amincewar kwamitin sulhu na majalisar, wajen ganin sun kara masa yawan dakaru guda dubu biyu a kasar Ivory Coast.

Ya ce ana bukatar karin dakarun ne domin su samar da kariya ga shedikwatar mutumin da kasahen duniya suka ce shine ya lashe zaben shugban kasar, wato Alasan Outtarra, wanda ke zaune yanzu haka a wani otal a birnin Abidjan.

Mr Lee Roy ya ce nan da wasu kwanaki masu zuwa zai shigar da kukansa ga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniyar.