Rahoton bincike ya soki kamfanonin man Amurka da yin sakaci

Malalar mai a kasar Amurka
Image caption Kwamitin binciken malalar man gabar tekun Mexico a kasar Amurka ya soki kamfanonin man Amurkan da yin sakaci.

Kwamitin da shugban kasar Amurka ya kafa ,domin gudanar da bincike kan matsalar malalar mai da ta auku a gabar tekun Mexico a bara ,ya ce lamarin ya faru ne saboda wasu matakai marasa kyau da kamfanin BP da kuma sauran kamafanonin suka dauka.

Kwamitin ya kuma yi gargadin cewa za'a sake samun aukuwar lamari irin haka, idan har ba'a gudanar da sauye sauye masu matukar muhimanci a kasar ba.

Dan Boesch mamba ne a kwamitin kuma ya yi wa BBC karin bayani inda ya ce an gano cewa babu wani takamaiman shirin kiyaye aukuwar duk wani bala'i daga wurin kamfanin BP da kuma abokanan aikinsa.

Kamfanin mai na BP dai ya yi watsi da sakamakon rahoton, yana mai cewa ya yi iya yinsa wajen takaita illar malalar man.