Sharhi kan rayuwar Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

Image caption Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, ya kasance mutum ne da ya yi fice da daukar hankalin jama'a matuka a lokacin rayuwarsa, a ciki da wajen Najeriya.

To, ko ya al'ummarsa ta Ibo take kallonsa? Mista Emmanuel Nzomiwu, wani mai sharhi kan al'amura ne da ke birnin Enugu, ya kwatanta marigayin a matsayin wani mutum da al'ummarsa ta Ibo ke kallo da kima da matukar muhimmanci, tare kuma da girmamawa. "Ojukwu Ibo ne wanda duk wani dan kabilar Ibo ya yi amanna da shi, kuma ya yi na'am da shi. Ibo suna kalllonsa ne a matsayin wani mutum dan kishin kasa, jagora mara son zuciya, mai fafutukar fitar da jama'arsa daga kangi, kuma mutumin da za su iya rugawa wajensa a lokacin damuwa." in ji Mista Emmanuel Nzomiwu. "Ba komai ya kai Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ga wannan matsayi ba, sai irin rawar da ya taka ga al'ummar tasa." A cewar Mista Emmanuel Nzomiwu

Marigayin ya yi fafutukar kwato yancin kabilar Ibo

Ya kara da cewa; "Muhimman bukatun dan kabilar Ibo shi ne abu mafi mhimmanci a wajensa. Don haka, kafin ka ji ya yi magana kan wani abu da ya shafi kasa, sai ya yi la'akari da inda ra'ayin Ibo ya karkata. Alkiblar da ya yi tsayuwar daka kanta kenan, ya yi ta fafutukar kwato wa jama'arsa hakkinsu." Mista Emmanuel Nzomiwu yana ganin rawar da Ojukwu ya taka a lokacin rayuwarsa, ba wai ga bangaren jama'arsa kadai ta tsaya ba. "Yana jin cewa, muddin ana son ingantuwar al'amura a Najeriya, tilas sai an karfafa tsarin dimokuradiyya a kasar. Don haka ne ma ya bi tafarkin siyasa mafi karbuwa a wajen jama'a. Kuma ya yi ta fafutukar tabbatar da daidaito da adalci da adala, gami da dayantakar kasar nan."

"Saboda haka na yi amanna cewa, Ojukwu ya bayar da gagarumar gudunmawa a fagen siyasar Najeriya." To, amma ya al'ummar Ibo ke kallon yadda marigayin ya jagorance su suka shiga yaki, kuma haka ba ta cimma ruwa ba? "Na yi imani cewa, shiga yakin da Ojukwu ya yi wani mataki ne na mayar da martani, don kare mutanensa, amma ba wai don kawai ya jefa su cikin rikici ko wani abu makamancin haka ba. " To, yanzu da yake Ojukwu ya kau, ko akwai wanda zai maye gurbinsa? A nan sai Mista Emmanul Nzomiwu ya ce: "Ba na jin haka, ko da yake muna da mutanen da ke tasowa, wadanda ke yin abin a zo a gani, amma kuma babu wani mutum da zai sami karbuwa wajen al'ummar Ibo kwata kamar Ojukwu. Saboda Ojukwu wani mutum ne da matsayinsa ya yi zarra."