Kamfanin Renault ya ce yana fuskantar barazana

Wani bangare na wata mota kirar Renault
Image caption Wani bangare na wata mota kirar Renault

Kamfanin kera motocin Renault na kasar Faransa ya ce, bayyanan sirrin da aka sata daga kamfanin, game da sabbin motoci masu amfani da lantarkin da yake kerawa, sun sa kamfanin na fuskantar babbar barazana.

A jiya an dakatar da wasu manyan manajokin kamfanin na Renault su ukku, bayan an kwashe wata guda ana gudanar da bincike.

Kamfanin Renault ya ce ya dauki matakin ne, domin ya kare mahimman kadarorinsa. Ya kuma zargi mutanen ukku da mika wasu manyan bayyanai na sirri, ga wani kamfanin da yake gogayya da shi, amma wanda bai bayyana sunansa ba.

A cewar ministan ma'adinan Faransar, Eric Besson, a yanzu kasar tana fuskantar yaki ta fuskar tattalin arziki.

Kamfanin Renault da abokin kawancensa na Japan, watau Nissan, sun kashe makudan kudade wajen gudanar da bincike game da motoci masu amfani da karfin wutar lantarki fiye da duk wani kamfani.