Saudiya ta kama wata Ungulun Isra'ila

100716130921_buitres_o_226x170.jpg
Image caption An dade ana zargin Isra'ila da yin leken asiri ta fannoni daban-daban

Rahotanni sun ce mahukunta a kasar Saudi Arabiya sun kama wata Ungulun Isra'ila bisa zargin tana yin leken asiri a kasar.

Ungulun wacce ke farauta tana dauke da wata na'ura da aka rubuta sunan jami'ar Tel Aviv, abinda ya haifar da zargin cewa manakisa ce ta Yahudawa.

Sai dai jami'an Isra'ila sun yi watsi da zargin, sannan suka nuna shakku kan makomar Ungulun.

Ungulun wacce fadin fikafikinta ya kai santi mita 265, an kama ta ne bayan da ta sauka a birnin Hyaal kwanaki kadan da suka gabata.

A lokacin da mazauna yankin suka gano na'urar ta GPS, sun yi zargi, sannan suka mika ta ga jami'an tsaro, a cewar jaridar Ma'ariv ta Isra'ila.

Nan take aka fara yada jita-jitar a jaridun Saudiyya da kuma shafukan intanet cewa ana amfani da tsuntsuwar ne wajen leken asiri.

Jami'an Isra'ila sun gayawa jaridar ta Ma'ariv cewa suna da damuwa kan zargin tare da tsoron hukuncin da tsutsuwar za ta fuskanta a hannun jami'an Saudiyya.

An dade ana zargin Isra'ila da yin leken asiri ta fannoni daban-daban, musamma a kasashen Larabawa.