Ouatara ya nemi ECOWAS ta dauki mataki kan Gbagbo

'Yan kasar Cote d'Ivoire suna zanga-zanga
Image caption Ko ECOWAS za ta amsa kira?

Mutumin da kasashen duniya suka amince cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar Kot Divuwa, Alassane Ouattara, ya bukaci kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, da su aike da dakaru na musamman domin tunbuke abokin hamayyarsa, Laurent Gbagbo, daga kan karagar mulki.

Mr Ouattara ya ce dole ne kungiyar ta ECOWAS ta dauki matakan da suka wajaba, wadanda suka hada da yin amfani da karfin da ya halatta.

Da yake magana ta wani gidan rediyon Faransa, Mr Ouattara ya jaddada cewa yana sa ran karbar ragamar iko a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa:

Ya ce, “Ni mutum ne mai son zaman lafiya, kuma watakila shi ne abinda ya sa magoya baya na suka zaku , suke ganin ya kamata mu gaggauta mu karbi iko.

To amma dai zamu kai can, ina da karfin guiwar cewa a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.”

A halin yanzu dai Babban Bankin Amurka ya ce ya haramta wa dukanin Amurkawa yin mu'amalar kudi tare da Mr Gbagbo da mukarrabansa.