Za'a yanke hukunci kan hana Atiku tsayawa takara

Image caption Atiku Abubakar

A Najeriya, kotun babban birnin tarayya ta tsayar da ranar Litinin, goma ga wannan wata na Janairu don yanke hukunci a kan karar da wasu 'ya'yan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar suka shigar suna neman jam'iyyar da ma hukumar zabe ta kasa su hana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar neman tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar.

Masu shigar da karar sun kafa hujjar cewa, kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, duk sun hana Atiku Abubakar tsayawa takarar shugabancin kasar saboda zargin da ake yi masa na cin hanci da rashawa.

Lauyoyi masu kare wanda ake karar dai sun nemi kotun ta yi watsi da karar, suna masu kafa hujja da cewa wadanda suka shigar da karar ba su da hurumin yin hakan a doka.

Atiku ya musanta zargin cin hanci

Masu shigar da karar, sun ce suna bukatar kotun da ta dakatar da Atiku daga tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam'iyyar PDP ne saboda a cewar su, hukumar kwastam ta kasa ta kori Atiku daga aiki ne saboda zarginsa da aikata ba dai-dai ba na cin hanci da rashawa, zargin da shi Atikun da lauyoyinsa suka musanta.

Haka zalika masu shigar da karar sun ce wani rahoton majalisar dattijan Amurka a shekarar 2010 ya samu Atiku Abubakar din da laifin aikata almundahana da safarar kudaden haramun a binciken da ya gudanar, batunda shi ma Atikun ya musanta.

Har wa yau masu shigar da karar suna bukatar kotun da ta bada umarnin a binciki Atiku Abubakar, bisa zargin karbar toshiyar baki a badakalar nan ta kwangilar Siemens ta hanyar mai dakinsa.

A don haka masu shigar da karar suka ce, korar Atiku da hukumar Kwastam ta yi daga aiki da kuma samunsa da laifin aikata almundahana da majalisar dokokin Amurka ta yi, sun isa su hana shi takara, saboda kundin tsarin mulkin PDP da na Najeriya sun hana duk wani mutum da ake zargin yana aikata laifuka daga tsayawa takara.

'Masu shigar da karar ba su da hurumin yin hakan'

Sai dai a nasu bangaren, lauyoyin dake kare Atiku Abubakar din sun ce masu shigar da karar ba su da hurumin yin hakan, kuma wasu daga cikin zarge-zargen da suke yi wa Atiku Abubakar din, tuni kotun koli ta wanke shi daga aikata su.

A ranar Litinin ne dai ake sa ran kotun zata yanke hukunci a kan ko za ta ci gaba da sauraron karar da kuma ko ma za ta kyale Atiku Abubakar din tsaya wa takara a zaben fidda gwani da jam'iyyar PDP za ta gudanar na wanda zai tsaya mata takara a zabe mai zuwa.

Idan ba a manta ba, kotun ta Abuja, ta sanya ranar Litinin din mai zuwa domin yanke hukunci a kan wata karar ta daban da wasu da ake ganin magoya bayan Atiku Abubakar din ne suka shigar, suna bukatar ta da ta hana shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga tsaya wa takara karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa.