Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Muhimmancin tsafta ga mace mai juna biyu

Image caption Akwai bukatar mayar da hankali wajen tsafta a lokacin dafa abinci

A cewar shafin internate na Wikipedia, tsaftar gida a rayuwar yau da kullum na da matukar muhimmancin gaske wajen kare yaduwar cututtuka masu yaduwa.

Kuma a cewar shafin abubuwan dake janyo yaduwar cututtuka sun hada da mutane, abinci, ruwa da kuma dabbobi.

Shafin na Wikipedia ya kuma bayyana cewa hanyoyin da cututtuka suke yaduwa sun hada da kayayyakin amfani na abinci kamar su cokula, ludaya da sauransu da kuma ta hanyar kayan sawa.

Kyakkyawar tsaftar gida dai na nufin kawar da kwayoyin cuta kafin su kai ga yaduwa. Kuma hanyoyin daukar kwayoyin cuta sun hada da hannuwa, ko ta cin wani abu, ko ta hanci ko ma dauka ta idanu.

A daya bangaren kuma tsaftar jiki a cewar Wikipedia kan janyo raguwar kamuwa da cuta, ko ma warkewa daga ciwo, samun koshin lafiya da hana bazuwar cuta ga wasu mutanen.

Shafin na Wikipedia dai ya nuna cewa zubar da shara a inda ya kamata da kula da muhalli da kuma dabbobi na da matukar muhimmanci a kasashe masu tasowa don kare yaduwar kwayoyin cuta.

Tsaftacaccen ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen tsaftar muhalli da kuma jiki. Don haka samar da wadataccen ruwa mai tsafta da samar da ababen kwashe bola na da matukar muhimmanci wajen kawar da cututtuka ma su yaduwa.

A shirye-shiryen Haifi Ki Yaye da BBC Hausa da suka gabata, an bayyana cewa kamuwa da wasu cututtuka da mata masu juna biyu ke yi na daga cikin manyan dalilan dake ci gaba da janyo mace-macen mata masu juna biyu a fadin duniya.

A wannan shirin mun duba batun tsaftar jiki da na muhalli a tsakanin mata, musamman masu juna biyu: