Ana binciken wani kampanin abincin Jamus

Masu gabatar da kara a Jamus na binciken wani kampanin hada abincin dabbobi, sakamakon gurbacewar da kwayaye suka yi da wani sinadari mai haddasa kamuwa da cutar sankara.

Wasu gwaje gwaje da aka gudanar kan wasu cimakar dabbobi sun nuna cewar suna dauke da sinadarin dioxin mai yawan da ya rubanya har sau saba'in da bakwai, adadin da aka amince.

Hukumomi sun ce mai yuwa kampanin na sane da wannan matsala tun cikin watan Maris na bara.

Yanzu haka dai akwai wasu gonaki kimanin dubu biyar a Jamus da aka haramtawa sai dai kayayyakinsu.