Jam'iyyar PDP ta lashe zaben jihar Delta

Shugaban Hukumar Zabe Attahiru Jega
Image caption Wannan zaben wani zakaran gwajin dafi ne ga Hukumar zabe ta Kasa

Dan takarar jam'iyyar PDP Dr Emmanuel Uduaghan, ya lashe zaben gwamnan da aka sake gudanarwa a jihar Delta dake yankin Niger Delta a Najeriya.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta bayyana cewa Dr Emmanuel Uduaghan ya lashe zaben ne da kuri'u 275,253, inda ya kada abokin hamayyarsa na kusa Great Ogboru na jam'iyyar DPP.

Jam'iyyu 14 ne dai suka fafata a zaben, wanda aka shirya sakamakon umarnin da kotu ta bayar na sake zaben.

Dama dai Dr Emmanuel Uduaghan ne aka zaba a zaben da gudanar a watan Aprilun shekara ta 2007.

An samu rahotannin sace-sacen kuri'u a wasu yankunan jihar, sannan an girke jami'an tsaro fiye da kima a sassa da dama na jihar.

Masana na yiwa wannan zabe kallon wani zakaran gwajin dafi, gabanin babban zaben da za a gudanar na kasa baki daya cikin watan Aprilun bana.

Karin bayani