Matsalar tashin bama-bamai a Nijeriya

Harin bam a Nijeriya
Image caption Harin bam a Nijeriya

A 'yan kwanakin nan dai za a iya cewa sha'anin tsaro a Nijeriya na kara tabarbarewa, musamman sabo da yawan kai hare-hare a sassa daban daban na kasar wadanda kan kai ga hasarar rayuka da dukiya.

Kwanakin baya ne aka kai hare haren bam a Jos, babban birnin jihar Pilato, lamarin da ya kai ga tashin hankali da asarar rayuka.

Kwanaki kadan bayan haka ne kuma bam ya tashi a wani barikin soja dake Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.

Hukumomi dai na cewa suna iya kokarinsu wajen magance matsalar ta kai hare-hare, inda ko a 'yan kwanakin nan rundunar 'yansandan jihar Borno ta ce ta kama mutane kimanin casa'in da biyu wadanda take zargi da kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram da kan kai hare-hare a jihar.

Sai dai duk da matakn da hukumomi ke cewa suna dauka, lamarin na ci gaba da faruwa.

Babbar tambaya ita ce, Me ya sa hare haren ke neman zama ruwan dare a Najeriyar? kuma Ina mafita?

A kan haka ne filin Ra'ayi Riga na yau ya tattauna tare da, Alhaji Sulaiman Abba, kwamishinan 'yan sanda na jihar Rivers, da Dr Bawa Abdullahi Wase, kwararre ta fuskar tsaro, kuma mai bincike kan harkokin tsaron bil'adama tare da jam'iar Oxford ta Ingila, wanda yanzu haka yake a Bauchi, da Dr Usman Bugaje, na jam'iyyar ACN, daga Katsina, da Hon. Ahmad Aliyu Wadada, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilai, kuma dan jam'iyyar PDP, daga Keffi a jahar Nasarawa.