Faransa za ta binciki fitar bayanan sirrin Renault

Samfurin motocin Renault
Image caption Samfurin motocin kamfanin Renault da ake takaddama a kai

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya bukaci hukumar leken asirin kasar da ta gudanar da bincike, kan zargin yin leken asiri a kamfanin kera motocin Renault.

Kamfanin na Renault ya dakatar da wasu manyan manajojinsa ukku, yana zarginsu da satar fasahar kera motoci masu amfani da karfin wutar lantarki.

Kamfanin yana kashe makudan kudade wajen kera irin wadannan motocin, a kokarin da yake na ganin ba kamar sa a shekaru masu zuwa.

Wasu majiyoyi a kamfanin na Renault sun yi amannar cewa, an tura bayanan da aka sata zuwa wani kamfani mai gogayya da shi a kasar China.

Ministan ma'adinan kasar Faransar ya bayyana zargin leken asirin da cewa, wani yaki ne ta fuskar tattalin arziki.