Ma'aikatar tsaron Amurka zata rage kashe kudi

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates
Image caption Ma'aikatar tsaron Amurka zata zaftare irin kudaden da take kashewa a sha'anin tsaro domin tunkarar gibin kasafin kudin kasa

Sakataren tsaron Amurka, Robert Gates ya ce zai zaftare kusan dalla biliyan tamanin daga cikin kasafin kudin sojin kasar nan da shekaru biyar masu zuwa.

Wannan dai shine mataki mafi girma da kasar zata dauka tun bayan harin sha daya ga watan satumpa na shekerar 2001.

Mr Gates ya ce matakin zaftare kudin ya zaman dole, saboda matsin da tattalin azikin kasar ke fuskanta.

Mr Gates ya ce yana kuma son ya jaddawa kawayen Amurkan cewar wannan mataki ba wai yana nufin Amurkan tana ja da baya bane dangane da irin rawar da take takawa a wasu kasashen duniya irinsu Iraki da kuma Afghanistan.