Koriya ta Arewa ta nemi a koma teburin shawara

Taswirar Koriya ta Arewa
Image caption Koriya ta Arewa ta nemi a koma kan teburin shawara domin a warware zaman zulumin da ake ciki a yankin

Koriya ta Arewa ta sake yin kira kan bukatar ganin cewa an koma teburin tattaunawa domin shawo kan zaman zulumin yankin, duk da cewa Koriya da Kudu da kuma Amurka sun aika mata da sakonin amincewarsu a tayin da tayi a baya.

Koriyar ta Arewar ta kuma ce zata sake bude ofishinta dake koriya ta Kudu a wata masana'antar hadin gwiwa dake iyakar kasashen biyu.

Sai dai Koriya ta Kudu ta rika yin watsi da kirayen da kirayen da Koriya ta Arewa ke yi mata a baya bayanan akan cewa ba komai bane illa far-faganda.