An sace 'yan kasar Faransa biyu a Nijar

Taswirar Nijar
Image caption Wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba dauke da makamai sunyi awon gaba da wasu Faransawa biyu a jamhuriyar Nijar

Wasu mutane dauke da makamai wadanda ba'a san ko su wanene ba, sun sace wasu 'yan kasar Faransa biyu a jamhuriyar Nijar.

Wadanda suka shaida lamarin da idanunsu sun ce an sace su ne a wani wurin cin abinci a Yammai babban birnin kasar, sanan aka wuce da su cikin wata mota

Daya daga cikin mutanen dai na shirin auren wata 'yar Nijar a makon gobe

Kungiyar Alqaeda dai ta sha gudanar da jerin sace sacen mutane a jamhuriyar Nijar, sai dai kuma ba'a taba sace 'yan kasashen waje ba a babban birnin kasar

A 'yan watanni ukun da suka gabata ma, wasu mayakan kungiyar AQMI ko kuma ALQAEDA sun sace wasu haifaffun kasar Faransan su 5 a yankin Agadez na arewacin Niger.